Shirin makamashin nukiliyar Iran
September 3, 2011Hukumar kula da makamashi ta Majalisar Ɗinkin Duniya IAEA, ta ce ta damu ƙwarai da wasu rahotannin sirrin da ta ke samu, waɗanda ke nuna cewa Iran na cigaba da ƙirƙiro makaman nukiliya a ɓoye. A wani rahoton da ta wallafa, hukumar ta ce ƙasashe mambobin ta da dama sun bayar da hujjoji da yawa dake bada tabbacin wannan batu. Rahoton dai ya kuma ƙara da cewa gwamnati a Tehran ta cika alƙawarin da tayi na canza wurin da ta sanya na'urar inganta ma'adanin uraniyum. Ita dai Iran ta ƙaryata wannan zargi kuma ta cigaba da ta kare hukumar daga gudanar da bincike dangane da wannan zargi na tsawon shekaru huɗu yanzu. Kwamitin Sulhun MDD ya sanya ma Iran takunkumi har huɗu sakamakon wannan zargi na sarrafa makaman ƙare dangi ko da yake Iran ta ce shirin makamashinta domin inganta fannonin da zasu taimaka wajen raya ƙasa ne.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal