Shirin makamashin nukiliyar Iran
February 18, 2012Babbar kantomar da ke kula da harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton da takwararta sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, sun yi maraba da tayin da Iran ta gabatar, na kaddamar da tattaunawa dangane da shirinta na makamashin nukiliya, bayan wata ganawa da Clinton a Washington na kasar Amurka, Ashton ta ce tana sa ran a wannan karon lallai gwamnati a Tehran zata komo teburin tattaunawa. A nata bangaren kuwa, Clinton ta yi godo da Iran da ta dauki matakin da zai kawo sulhu a rikicin nukiliyar tun da dai ta bayar da kai ga tattaunawar.
"Wannan martani da muka samu daga gwamnatin Iran, shi ne muka dade muna jira, kuma idan har muka cigaba, dole ne ya zama wani yunkuri mai dorewa wanda kuma zai bada sakamako mai kyau".
Babban mai shiga tsakani kan batutuwan makamashin Nukiliyar na Iran Saeed Jalili -ya gabatar da bukatar sake kaddamar da wannan tattaunawa nan bada dadewa ba, a wata wasikar da ya aikawa Ashton. To sai dai kasashen yamma na zargin Iran da kokarin sarrafa makaman kare dangi abun da Iran ta karyata.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Umaru Aliyu