Shirin nukiliya a IRAN
January 4, 2011ƙasar Iran ta gayaci jakadun ƙasashen duniya a ciki har da na China da kuma Rasha domin kai ziyara gani da ido a cibiyoyin samar da makamashin nukliya na ƙasar, a wani yunƙuri na bada hadin kai ga bincikar shirinta na nukliya.Mai magana da yawun ofishin ministan harkokin waje na ƙasar ta Iran Ramin Mehmanparast ya ce sun gayyaci ƙasashen yammancin duniya da dama, gabanin taron tattaunawa akan shirin nukiliyar na ƙasar da za a yi a ƙarshen watan Janairu a birnin Samtambul.
Taron wanda za a yi tare da ƙasashe guda biyar masu kujeru dindindin a Majalisar ɗinkin Duniya, tare da Jamus na zaman wata hanya ta warware takaddamar da ake yi tsakanin Iran da ƙasashen yammancin duniyar dake zarginta da yin amfani da makamashin don kera makamai masu dogon luzami abinda ƙasar take musuntawa :
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi