Shirin nukiliyar Iran na ƙara shan suka
March 13, 2010Tarayyar Daular Larabawa ta ce a shirye take ta mutunta sabon takunkumi karya tattalin arziki da Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai ƙaƙabawa ƙasar Iran. Sanarwa wacce ministan harkokin waje na ƙasar Abdallah Ben Zayed Al- Nahyane ya baiyana a daidai lokacin da ake cikin tankiyar, na zaman wani kware bayan ƙasashen Larabawa ga ƙasar Iran. To sai dai mista Zayed ɗin ya ce ya na fatan kafin a kai can, ƙasar Iran za ta amince a kai ga warware matsalar ta hanyar tattaunawa ta dilplomasiya. A 'yan kwanakin baya bayan nan dai sakataren tsaro na Amerika Robert Gates ya kai ziyara a cikin ƙasashen yankin Tekun Pasha, domin samun goyon bayan ƙasashen akan sabbin takunkumi da ake shirin sakawa ƙasar Iran. Ƙasashen yamma dai na zargin hukumomin Iran da ƙoƙarin ƙera makaman nukiliya, to amma mahukuntaa birnin Teheran sun ce shirin inganta sinadarin Uranium da ƙasar ke yi na samar da hasken wutar lantarki ne.
Mawallafi: Abdurrahman Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal