Shirin nukiliyar Iran
July 23, 2015Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya kare yarjejeniyar nukiliyar da kasarsa ta cimma tare da Turai, inda ya soki masu ra'ayin mazan jiyan kasar wadanda ke nuna adawa da sabon matakin, yana mai cewa yarjejeniyar ta bayyana abin da 'yan kasar ke muradi ne, kuma wannan ya fi mahimmanci a kan cece-kucen cikin gida dangane da gundarin abin da yarjejeniyar ta kunsa.
Bisa bayanan kamfanin dillancin labaran Reuters dai, sojojin juyin juya halin kasar wadanda suke da tasiri sosai a batutuwan siyasa da tattalin arziki da tsaron kasar ne, suka fi sukan shirin, da hujjar cewa babban hatsari ne ga tsaron Iran.
A karkashin wannan yarjejeniya ta 14 ga watan Yuli, za a rika janyewa Iran takunkumin da aka kakaba mata sannu a hankali, a yayin da a waje guda kuma ake kokarin takaita shirinta na makamashin nukiliya wanda tun da dadewa Turai ke zargin cewa na hada-hada makaman kisan kare dangi ne, zargin da ta karyata.