A cikin shirin za a ji cewa mahukunta Jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da wani harin da ya jikkata jama'a da dama a jihar Tillabery. A Najeriya, dattawa kasar ne ke ci-gaba da sam-barka kan yadda kasar ke cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan bayyana sakamakon babban zaben Najeriyar na 2023.