A cikin shirin za a ji cewa, a Najeriya ana ci gaba da mayar da martani kan rabon ma'aikatu da aka yiwa ministoci da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada. A Jamhuriyar Nijar, gomman fararen hula ne suka mutu sakamakon sabbin hare-hare da ‘yan ta’adda suka kai a wasu kauyika jihar Tillabery.