1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin rusa majalisar dokokin Senegal

Usman Shehu Usman
September 4, 2024

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya kammala shirin rusa majalisar dokokin kasar wacce 'yan adawa suka fi rinjaye kana gwamnatinsa ta kaddamar da bincke kan cin-hanci ga jami'an gwamnati.

https://p.dw.com/p/4kHfG
Senegal Parlament in Dakar
Hoto: Carmen Abd Ali/AFP/Getty Images

Firaministan Senegal Ousmane Sonko wanda ya furta haka a wannan Larabar, ya fadi hakan ne kwana guda bayan da 'yan adawa masu rinjaye a majalisar dokoki suka yi watsi da wani kuduri da gwamnati ta gabatar, batun da gwamnatin Bassirou Diomaye Faye,  ke ganin cewa kawancen tsohon shugaba Macky Sall ne suke neman jijjiga gwamnatinsu. Dama dai Ousmane Sonko wanda ke zama Firaminista da kuma Bassirou Diomaye Faye sun yi nasarar lashe zaben kasar Senegal ne bayan da suka jagoranci mummanan adawa hadi da tarzuma wa gwamnatin Macky Sall, inda a lokacin suka yi wa 'yan kasar na samu gagarumin canji da zaran sun hau kan mulki. To amma kawo yanzu 'yan kasar Senegal basu kai ga ganin wadancan alkawura da aka yi musu ba, duk da cewa Sanko da Bassirou Diomaye Faye sun samu nasarar hawa kan mulkin.