A cikin shirin za ku ji cewar babbar cibiyar bincike ta musulunci ta gargadi musulmin duniya a kan su daina bijirewa dokokin da gwamnati ke sawa a kasashensu don yaki da cutar coronavirus, a daidai lokacin da kasar Masar ta sanar da karin albashi mai tsoka ga likitocinta masu aikin kawar da cutar Corona.