Shirin ya kunshi rahotanni da labaran duniya har da yadda Firaiministan Burkina Faso Christophe Joseph Marie Dabire da gwamnatinsa suka yi murabus wanda ya kasance karon farko a nahiyar Afirka da shugaban gwamnatin da mambobin majalisar ke yin marabus saboda matsin lamba daga al'ummar kasar.