Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewar kasar Burundi ta fara yi wa jami'an lafiya da ke aiki a iyakar kasar da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango rigakafin cutar Ebola, cikin shirin kare lafiyar jami'an daga barazanar kamuwa da zazzafan zazzabin Ebola mai saurin kisa.