1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNijar

Jamhuriyar Nijar: Sake rubuta tarihin kasa

Salissou Boukari LM
November 21, 2024

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun kudiri aniyar sake rubuta tarihin kasar, sabanin tarihin da Turawan mulikin mallaka suka rubuta. Sai dai wasu na ganin, inganta fannin ilimi da mulki na gari kasar ke fatan samu.

https://p.dw.com/p/4nI6j
Jamhuriyar Nijar, Tarihi
Kasashen Afirka na da dadadden tarihiHoto: mzuuzu/Pond5/IMAGO

Wani kwamiti ne gwanatin ta kafa da zai yi nazarin sake tarihin Jamhuriyar ta Nijar, a karkashin jagorancin Farfesa Maikoréma Zakari da kuma ya kunshi malaman jami'a da dama.  Akwai yiyuwar kwamitin zai bukaci manyan masanan tarihi da masu bincike a kasar, su kawo tasu gudunmawar. Wannan mataki da shi ne na farko na da burin sake nazari da kuma rubuta tarihin Nijar daidai da kasar da aladunta, ganin cewa an bayyana tarihin da aka yi ta koyarwa a makarantun kasar Turawan mulkin mallaka ne suka rubuta daidai yadda suke son ya kasance. Da yake tsokaci kan wannan batu malami a jami'ar birnin Damagaram Dakta Gambo ya ce, sanin cikakken tarihin abu ne mai kyau sai dai kuma kar fa a yi ciwo dabam magani dabam. Sai dai kuma a nasa nazarin Atto Namaiwa  da ke zaman malami a jami'ar birnin Tahoua ya ce, abun da zai fi babban tasiri shi ne sanin al'adun dukannin kabilun kasar ta Nijar ta yadda hakan zai taimaka wajen warware wasu matsaloli har ma da na fannin shari'a. Ya zuwa yanzu dai kallo ya koma ga wannan kwamiti, domin ganin yadda masanan da ke cikinsa za su yi la'akari da tsarin kabilun kasar da ma harsuna ta yadda sakamakon aikin da za su fitar zai taimaka wajen hada kawunan 'yan kasar ba wai saka rudani ba.