1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin SPD na kalubalantar Merkel a 2013

Halimatu AbbasSeptember 29, 2012

Jam'iyar SPD mai adawa a Jamus ta gudanar da babban taronta inda dan takarar ta Peer Streinbruck ya ce ya na da yakinin kai labarai a lokacin da zai kalubalanci Merkel a 2013.

https://p.dw.com/p/16Hba
Nordrhein-Westfalen/ Der designierte Spitzenkandidat der SPD fuer die Bundestagswahl 2013, Peer Steinbrueck, spricht am Samstag (29.09.12) in Muenster beim Parteitag der nordrhein-westfaelischen SPD. Auf der Tagesordnung des Parteitags steht unter anderem die Neuwahl des Landesvorstandes. (zu dapd-Text) Foto: Sascha Schuermann/dapd.
Peer Steinbrück zai tsaya karkashin jam'iyar SPDHoto: Sascha Schuermann/dapd

 Dan takarar da jamiyar adawa ta SPD ta tsayar  a zaben gama gari da zai gudana a shekara mai zuwa a Jamus Peer Steinbrück  ya ce  jam'iyar ba zata yi kawance da ta CDU dake mulki ba  in har ta sha kayi a zaben da zai gudana shekara mai zuwa.  Steinbrück ya ce ba  zai fuskanci taranaki wajen cimma manufofinsa a duk wata  gwamnati  da Angela Merkel zata jagoiranta. 

Ya fadin haka ne  a babban taron da jamiyarsa ta SPD ta gudanar a garin Münster  dake nan jihar Nordrhein Westphalen.  Steinbrück ya kuma jaddada cewa babu wata baraka da za a samun tsakanin shi da Sigmar Gabriel  da Frank Walter  Steinmeier dake jan ragamar jam'iyar.

Mawallafi: Halimatu Abbas
Edita: Mouhamadou Awal