Shirin tattauna rikicin gabashin Ukraine a birnin Minsk
February 11, 2015Talla
Da farko dai Shugabar Gwamnatin Jamus zata yi wata ganawa da shugaban kasar Faransa da na Ukraine, kafin shiga zauran babban taron inda zasu tattauna da shugaban Rasha Vladmir Putin. Wannan dai ita ce ake gani a matsayin haduwa ta sa'ar karshe kan wannan rikici na Ukraine wadda mundin ba'a samu cimma wata yarjejeniya ba.
Shugaban kasar Belarus Alexandre Loukachenko ya tarbe su daya bayan daya yayin da suka sauka a birnin na Minsk. kawo yanzu dai rikicin gabashin kasar ta Ukraine ya yi sanadiyar rasuwar mutane a kalla 5.300, yayin da wasu dubunnai suka bar matsugunnansu.