1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tsagaita wuta a Siriya ya gaza yin tasiri

Abdourahamane HassaneApril 28, 2016

Manzon Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a Siriya Staffan de Mistura ya yi kira ga shugaba Vladmir Poutine na Rasha da Barack Obama na Amirka da su ceci shirin tsagaita wuta a Siriya.

https://p.dw.com/p/1IeRG
Genf Friedensgespräche zu Syrien - Staffan de Mistura
Hoto: Reuters/D. Balibouse

Staffan De Mistura ya bayyana faRgabansa game da irin yadda ake samun ƙaruwar tashin hankali a ƙasar amma kuma ba tare da samun hanyoyi kawo ƙarshen rikicin ba.A jiya an watse baraM-baram a taron tattaunawar na Geniva wandan 'yan adawar na Siriya suka janye sakamakon ƙorafin da suka yi cewar gwamnatin Bashar al Assad na ci gaba da kashe fararan hula.

Hakan kuwa na zuwa ne a daidai loksai da aka ba da rahoton cewar mutane aƙalla guda 20 a ciki har da yara a likitoci,sojojin Siriya suka kashe a sakamakon wani farmaki da jiragen sama na yaƙi kai a kan wani asibiti a arewa maso yammaci birni Alepo.