Masar ta ayyana zaman makoki sakamakon mutuwar kimanin mutane 235 da jikkatar wasu gwammai, bayan wani harin ta'addancin da aka kai wani masallacin Juma'a a arewacin yankin Sinai, harin da shi ne irinsa mafi muni da aka taba kaiwa wajen ibada a kasar.