A cikin shirin za a ji cewa, hukumomi sun ce kimanin mutum 50 aka tabbatar da mutuwarsu, wasu gommai kuwa suka jikkata sakamakon zanga-zangar adawa da sabuwar gwamnatin riko. Ita kuwa gwamnatin Masar ta kammala shirin kaurar da babban birnin kasar daga Alkahira zuwa wani sabon wuri a tsakiyar Hamada.