1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

May 24, 2013

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na ganawa da shugabannin Isra'ila da na yankin Palesdinu domin tsayar da lokacin komawa kan teburin sulhunta rikicin yankin.

https://p.dw.com/p/18dE5
Hoto: picture alliance/AP Photo

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na ci gaba da ziyarar aiki ta hudu da ya ke gudanarwa a yankin gabas ta tsakiya cikin watannin hudun da suka gabata. Bayan da ya gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Kerry ya ce ya kwana da sanin cewar akwai shakku da ke tattare da zukantan kasashen yankin dangane da rikice rikice da ke addabarsu.

Sakatare na harkokin wajen Amurka ya yi alkawarin tsayawa tukuru domin ganin cewar an warware takaddamar da ke tsakanin Isra'ila da kuma yanin palesdinu. Bisa ga kafofin watsa labaran Isra'ila dai akwai yiwuwar farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin bani yahudu da kuma palesdinawa a farko farkon watan Yuni. Bayan da ya gana da shugaban Isra'ila Shimon Peres, John Kerry ya isa Ramallah domin tattaunawa da shugaban palesdinawa Mahmud Abbas.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu