Shirin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
July 16, 2010Jam'iyar Fatha ta shugaba Mahmoud Abbas ta nuna shakku game sakamakon da tattaunawa gaba da gaba tsakanin Palesdinu da Isra'ila za ta haifar. cikin wata sanarwa da ta wallafa, Fatha ta ce ba ta ganin cewa wannan salon samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, zai samar da wani abin kirki sakamakon munanan muaradun gwamantin Isra'ila.
Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da manzon musammun na Amirka a yankin Gabas ta Tsakiya wato George Mitchel ya koma yankin, da nufin gano bakin zaren warware rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Isra'ila da kuma Palesɗinu. A wannan juma'a Mitchel zai gana da firaministan Isra'ila wato Benjamin Netanyahu. A Gobe asabar kuma zai sadu da shugaba Mahmoud Abbas na Palesɗinu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou