1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen taron Annapolis a game da rikicin Gabas ta Tsakiya

Yahouza Sadissou MadobiNovember 23, 2007
https://p.dw.com/p/CSRa

A shiryen-shiryen taron Annapolis, wanda Amirka ta gayyata akan rikicin gabas ta Tsakiya, ministocin harakokin waje na ƙungiyar ƙasashen larabawa, na ci gaba da zaman taro a birnin Alƙahira.

Ƙungiyar na da burin cimma matsaya ɗaya a game da taron na Annapolis.

Ministocin sunyi kira ga Amirka, ta saka batun tudan Golan a ajendar wannan taro.

Syria tace ba zata halarci ganawar ta Annapolis ba, muddun babu batun na Tudan Golan ,da Isra´ila ta mamaye mata.

A yayin da ya ke jawabi, jim kaɗan kamin buɗe taron na Alƙahira, Sakatare Janar na ƙungiyar haɗin kann larabawa Amr Musa, ya kyauttata zaton taron Annapolis ya zama sanadiyar gikuwar zaman lahia mai ɗorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.