1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zabe a kasar Togo

Lina HoffmannJuly 24, 2013

'Yan adawan Togo sun yi korafi game da magudi tun ma kafin a gudanar da zaben da ake sa ran jam'iyar UNIR ta shugaba Faure Gnassingbé za ta lasheshi.

https://p.dw.com/p/19DV7
Hoto: picture alliance/AP Photo

Zaben na kasar Togo zakaran gwajin dafi ne mizanin mulkin demokaradiya da fadar mulki ta Lome ta ke ikirarin bi. Sai dai tuni aka riga aka yi hasashen jam'iyar da za ta lashe shi, wace ba wata ba ce illa UNIR ta shugaban Faure Gnassingbé. Saboda haka ne Fabbi Kouassi, ma'abociyar amfani da hanyar sadarwa ta zamani wato Blog ta ke danganta da shi da na jake na yi ka.

"Ba wani abin da na ke jira daga wannan zabe. Hukumar da ke kula da harkokin zabe, karen farautar jam'iyar da ke mulki ne. Kotun tsarin mulkin kasar ma, 'yar amshin shatar gwamnati ce. ka da ma ayi wani mafarki. Ba zabe ne da za a gudanar da shi cikin adalci ba. Zabe ne da aka riga aka murdashi."

Ita dai Fabbi Kouassi ta na daga cikin wadanda suke amfani da bakin alkalaminsu wajen nuna rashin amincewarsu da yadda al'amura ke gudana a Togo. A shafinta na Blog ta yi tir da kamun ludayin shugaba Faure Gnassingbe musamman ma samun gindin zama da cin hanci da kuma tauyen hakkin bil Adama suka yi a cikin gwamnatinsa. Ko da ita ma Kouassi an yi ta  barazanar hallakata ta wayar tarho.

Togo Jean-Pierre Fabre Opposition 07.06.2013
Ba alamun jam'iyar Jean-Pierre Fabre za ta yi nasara a zabenHoto: Daniel Hayduk/AFP/Getty Images

Babakeren dangin Gnassingbe a fagen siyasa

Zaben na 'yan majalisar Togo ya kama hanyar ba wa iyalin Gnassingbe damar ci-gaba da cin karensu ba tare da babbaka ba. Shi dai shugaba mai ci a yanzu Faure Gnassingbé ya dare kan kujerar mulki ne shekaru takwas da suka gabata, bayan rasuwar mahaifinsa Gnassingbé Eyadema wanda ya kakkange harkokin mulkin Togo tun shekarar 1967. Kasar da ke yammacin Afirka na daya daga cikin wadanda suka fi talauci a duniya. AlKaluma da bakin raya kasashen Afirka ya fitar sun nunar da cewa kashi daya bisa uku na matasan Togo na fama da zaman kashe wando. Sannan kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kashi daya bisa biyu na al'umar kasar ba su iya karatu da rubutu ba.

A cewar Ralf Wittek, shugaban reshen gidauniyar Hanns-Seidel ta Jamus da ke Burkinsa Faso, wanda kuma ya yi farin sanin Togo, jam'iyun adawan wannan kasa ma na da na su laifin, inda su gaza share wa dimbin 'yan Togo hawaye. Saboda haka ne ma gidauniyarsa ta girka wani shiri na ilimantar da jama'a a wannan kasa.

"Dangin Gnassingbe na amfani a duk fadin kasar da dabaru iri daban daban wajen tabbatar da karfin fada a jinsu. Sauran jam'iyu siyasan na fama da rarrabuwar kawuna, lamarin da ya zame musu karfen kafa wajen daukan matakan da suka dace. Ko da bangaren da ke mulki ya fuskanci kalubale a zaben, 'yan adawa ba za su kai labari ba, saboda kawunansu ba a hade su ke ba."

Togo Faure Gnassingbe Präsident Archivbild 15.05.2013
Tun 1967 iyalin Gnassingbe ke mulki a TogoHoto: Georges Gobet/AFP/Getty Images

Wasu 'yan Togo sun juya wa zaben baya

Tsofuwar gamayyar Jam'iyun adawan kasar ta Togo wato UFC ta shiga cikin gwamnatin hadin gambiza da Faure Gnassingbe ya kafa tun shekaru ukun da suka gabata. Sai dai wasu Kusoshin gamayyar sun nesanta kansu daga wannan yunkuri, tare da kafa wata sabuwar jam'iya mai suna Alliance pour le Changement. A halin yanzu ma dai ita AFC ce jam'iya daya tilo da ke da rassa a duk fadin kasar ta Togo. Sannan kuma ta na sahun gama na Jam'iyun adawa da suka fi samun karbuwa a kasar. Sai dai kuma fatan da jam'iyun adawa ke da shi na taka rawar a zo a gani a zaben bai taka kara ya karya ba. Dalili kuwa shi ne, da yawa daga cikin 'yan Togo za su kaure wa zaben na 'yan majalisa domin nuna bacin ransu da rashin kwaskware dokokin da suka shafi zabe da gwamnati ba ta yi ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman