1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake fursunoni sama da 500 a Masar

Abdul-raheem Hassan
May 17, 2019

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya yafe wa fursunoni 560 da ke tsare a gidan yari bisa zargin laifuka daban-daban, ciki har da sanannun 'yan jaridu da wasu mata da aka kama lokacin boren kin jinin gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/3IfVl
Ägypten Präsident Abdel Fattah al Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/V. Belousov

Afuwar fursunonin ta zo ne a cikin watan azumin watan Ramadan, watan da yawancin shugabannin kasashen Musulmi ke yafe wa fursunoni da ke jiran shari'a. Sai dai wasu rahotanni na cewa an saki wasu 'yan jaridu saboda fama da rashin lafiya. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na Allah wadai da yadda gwamnatin Masar ke gallazawa 'yan adawa da 'yan jaridu.