1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta nemi zurfafa bincke kan asalin corona

May 27, 2021

Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya bukaci hukumar tattara bayanan sirrin kasar ta sake rubanya bincikenta wajen gano asalin yadda kwayar cutar Covid-19 ta baiyana.

https://p.dw.com/p/3u1d3
Konflikt in Nahost | Waffenruhe zwischen Israel und Gaza
Hoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

Amirka ma dai ta bi sahun kasashen duniya wajen matsa wa China lamba don fitar da sahihin bayani kan asalin bullar cutar. Tuni dai shugaba Biden ya umurci manyan dakunan binciken kimmiyar Amirka su tallafa wajen gudanar da binciken na kwakwaf kana ya bukaci hukumomin su bashi rahoto nan da kwanaki 90.

Shugaban ya kuma yi kira ga China ta bada cikakken hadin kai ga binciken na kasa da kasa game da asalin cutar. Rahotannin na nuna cewa cutar ta Coronavirus da ta bulla a karshen shekarar 2019 ta samo asali ne daga wani dakin bincike na China yayin da masana ke cewa cutar ta samo asali ne daga dabbobi suka kuma yadata ga mutane.