Shugaba Erdogan ya gana da Shugaban Faransa
January 5, 2018
Da yake jawabi yayin taron shugaba Macron ya ce kawai bukatar a da da duba batun kasar Turkiyya na zamowa mamba a kungiyar Tarayyar Turai.
A nasa bangaren Erdogan ya bayyana tsaikon da kasar sa take samu na zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai da cewa wani abu ne da ita kanta Kungiyar tarayyar Turai bata da Hujja ko dalili na kin amincewa.Shi dai Erdogan yana cigaba da fitowa fili ya nuna adawa da duk manufofin Amirka tun bayan da Donald Trump ya amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.
A wani cigaban kuma Erdogan ya zargi kasashen Amirka da Israila da yin kutse cikin al'amuran gudanarwar kasar Iran dake makotaka da kasar ta Turkiyya.
Ya zuwa yanzu dai mutane 21 ne suka rasa rayukansu yayinda aka kame daruruwan Jama'a sakamakon Zanga zangar dake zaman wani babban kalubale ga shugabancin kasar na Islama tun bayan hatsaniyar da kasar ta taba tsintar kan a ciki a shekara ta 2009.
Erdogan ya shaida wa manema labarai a yau yayin da yake shirin kai ziyarar aiki kasar Faransa cewar ba zasu laminci wasu kasashe su sa baki a harkokin cikin gidan kasashen Iran da Pakistan ba musammam ma Amirka Isra'ila kasashen da ya bayyana da cewar sune suka haddasa rikici a kasar Iraq.
Shi dai Erdogan yana fitowa fili ya nuna adawa da duk manufofin Amirka tun bayan da Donald Trump ya amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.