Shugaba Erdogan ya zargi Amirka da Isra'ila
January 5, 2018Talla
Shugaba Racep Tayyip Erdogan na sukar duk manufofin kasar Amirka ne tun bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila. Erdogan ya shaida wa manema labarai a yau yayin da yake shirin kai wata ziyarar aiki kasar Faransa cewar ba za su lamunci wasu kasashe su sa baki a harkokin cikin gida na kasashen Iran da Pakistan ba, musammam ma kasashen Amirka Isra'ila wadanda ya bayyana da cewar su ne suka haddasa rikici a kasar Irak.
Ya zuwa yanzu dai mutane 21 ne suka rasa rayukansu yayin da aka kame wasu daruruwan jama'a sakamakon zanga zangar da ta kasance kalubale ga shugabancin kasar ta Iran, tun bayan hatsaniyar da ta biyo bayan babban zabe a shekara ta 2009.