Ziyarar bazata a masallacin Paris
January 10, 2016Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya kai wata ziyarar bazata a babban masallaci da ke birnin Paris a ranar Lahadin nan, shekara guda bayan harin 'yan jihadi a birnin da ke zama fadar gwamnatin Faransa.
A cewar fadar gwamnatin ta Faransa shugaban ya tattauna da ma shan shayi da mahalarta masallacin.
Tun da fari dai sai da shugaban ya ziyarci wasu shirye-shirye na tunawa da wadanda suka rasu a lokacin harin da aka kai gidan jaridar Charlie Hebdo da wani katafaren shagon Yahudawa.
Al'ummar wannan kasa dai na cikin juyayi na tunawa da wannan rana ta 11ga watan Janairu 2015, da ke zame musu ranar tunawa da 'yan fadin albarkacin baki a fadar Jean Pierre Musli da ke zama mazaunin birnin na Paris.
'Wannan na tuna mana da mutanenmu da suka rasu a fafutika ta fadin albarkacin baki , wanda shi ke zama abin da Faransa ke alfahari da shi".