Shugaba Lula ya ki karbar goron gayyata
May 26, 2023Talla
Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil ya yi watsi da tayin takwaransa na Rasha Vladimir Putin, kan ya halarci taron kolin kasashe masu karfin tattalin arzikin masana'antu na na duniya G7 da za a yi a birnin Saint-Pétersbourg a tsakiyar watan gobe.
A cikin wata tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, Shugaba Lula ya bayana cewa ba zai halarci taron na kasar Rasha ba a halin yanzu, sai dai ya kara da cewar kasar Brazil tamkar sauran takwarorinta irinsu India da Chaina da Indunisiyya, a shirye take domin sulhunta rikicin da Rashar ke yi da makwabciyarta Ukraine.
Daman dai can a baya shugaban na Brazil ya kasa haduwa da takwaransa na Ukraine a babban taron kungiyar G7 da aka gudanar a baya.