Shugaban Zambiya ya amince da shan kaye
August 16, 2021Shugaban Zambiya mai barin gado Edgar Lungu ya amince da shan kaye tare da taya abokin hamayyarsa na tsawon lokaci Hakainde Hichilema, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da gagarumar nasara murna. Shugaba Lungu, bayan shan kaye yayi alkawarin daraja wa tanadin kundin tsarin mulki domin musayar mulki cikin ruwan sanyi.
Tsohon jagoran adawa Hakainde Hichilema ya lashe zaben shugaban wannan kasa ta yankin Kudancin Afirka, bayan samun sama da kaso 50 daga cikin 100 na yawan kuri'u da aka kada. Da safiyar wannan Litinin ne, shugaban hukumar zaben Zambiya Esau Chulu ya sanar da sakamakon mazabu 155 daga cikin 156 da ke fadin kasar.
Wannan shi ne karo na shida da fitaccen dan kasuwa Hichelima mai shekaru 59 da haihuwa, ya yi takarar kujerar shugabancin kasar ta Zambiya inda yayi nasarar samun kuri'u sama da miliyan biyu da dubu dari takwas, a yayin da abokin takararsa kuma Shugaba Edgar Lungu ya samu yawan kuri'u miliyan daya da dubu dari takwas.
Lamarin ya sa zaben na wannan karon zama mai cikakken tarihi a kasar da ke a yankin Kudancin Afirka. Rahotanni na nuni da cewar Hichilema ya samu sama da kaso 50 na kusan kuri'u miliyan biyar da aka kada, wanda baya bukatar tafiya zagaye na biyu na zaben. A zabukan shekarar 2015 da 2016 ya sha kaye da 'yan kuri'u kalilan wa abokin takararsa Shugaba Lungu mai barin gado. Sai dai sannu a hankali ya cigaba da samun karin goyon baya na amincewar al'ummar ta Zambiya.
Shugaba Lungu da ke kan karagar mulki tsawon shekaru shida, yayi kokarin zarcewa, duk da matsi na tattalin arziki da ya jagoranci tashin farashin kayayyakin masarufi. Hichilema, wanda ya ke da digiri a fannin tattali ya yi alkawarin sake janyo hankalin masu zuba jari na ketare zuwa wannan kasar da ke fama da faduwar darajar kudi, ga basussuka da rashin aikin yi.