Shugaba Maduro zai karbi sakamakon zabe da hannu bibbiyu
July 28, 2024Al'ummar kasar Venezuela na kada kuri'a a zaben shugaban kasa wanda sakamakonsa ka iya kawo sauyi a cikin shekara shida ko kuma ci gaba da manufofin shugaba Nicolas Maduro.
Duk wanda ya lashe zabe tsakanin Mista Maduro da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon ma'aikacin diflomasiyya Edmundo Gonzalez, nasarar za ta yi tasiri a nahiyoyin Amurka.
Rikici tsakanin Trump da Maduro
Magoya baya da kuma 'yan adawar gwamnati da dama sun nuna alamar tserewa daga kasar su shiga kasashen duniya don neman damarmaki. A halin yanzu akwai 'yan Venezuela sama da miliyan 7.7 da suke kasashen ketare.
Tawagar kwararrun zabe za ta je Venezuela
Babban abokin hamayyar Maduro Mista Gonzalez ya sha alwashin bibiyar yadda zaben ke gudana domin tabbatar da an yi adalci.