1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Shugaba Mahama ya karbi ragama

January 7, 2025

John Dramani Mahama ya sha rantsuwa a matsayin sabon zababben shugaban kasar Ghana, bayan gagarumar galabar daya samu a zaben watan Disamabar shekara ta 2024 da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4ovBc
Ghana | Shugaban Kasa | John Dramani Mahama
Sabon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama yayin rantsuwar kama aikiHoto: NIPAH DENNIS/AFP/Getty Images

Kakakin majalisar dokokin Ghana Alban Sumana Kingsford Bagbin ne dai, ya bayar da umarnin rantsar da sabon shugaban kasar John Dramani Mahama. Idan har ba tare da ya bayar da wannan izini ba, to ba za a iya rantsar da shugaban kasa a Ghana ba. Sabon shugaban na Ghana John Dramani Mahama ya sha rantsuwar kama mulki ne a karo na biyu, bayan an rantsar da mataimakiyarsa da ke zaman mace ta farko da ta taba rike wannan mukami a Ghana Farfesa Nana Jane Opoku Agyemang. Bayan ya sha rantsuwar kama mulkin, sabon shugaban ya kara jaddada wa jama'ar kasar cewa zai yi gaskiya ya kuma kare kundin tsarin mulkin Ghana a koda yaushe. Ya kara da cewa, ya sadaukar da kansa ga hidima da tsare jama'ar Ghana a koda yaushe kuma in har ya saba zai gabatar da kansa ga dokokin Ghana ya kuma mika wuya ga duk hukuncin da ya biyo baya.

Ghana | Nana Akufo-Addo | Najeriya | Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban Ghana Nana Akufo-AddoHoto: State Hause Abuja

A jawabinsa yayin rantsar da sabon shugaban kasar ta Ghana, takwaransa na Tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya kasance babban bakon da ya fara bayani ya ce wannan biki na dorewar dimukuradiyya ne a Afirka. Ya kara da cewa ba kawai alama ce ta wani ci-gaba ba a bunkasar dimukuradiyyar Ghana ba, wannan ya kara nuna cewa a yammcin Afrika za a iya kwatancen ayyukan dimukuradiyya da ayyuka na ci-gaba. Shugabannin kasashe 21 ne suka hallarci taron tare da suka hadar da tawagar shugaban Amurka da Beljiyam da Afrika ta kudu da Paul Kagame na Ruwanda da wasu shagabannin Afrika da suka hada da tsofaffi kamar Olesugun Obasanjo da Goodluck Jonathan da wakilan jakadancin kasashen duniya da dama.