Shugaba Mahmud Ahmadinedjad ya gana da takwaransa na Nijar
April 15, 2013Shugaban Kasar Iran Mahmud Ahmadinedjad ya isa Nijar a ci gaba da ziyarar kwanaki uku da yake a yankin Afrika ta yamma.
Nijar dai ta Kasance kasa ta hudu a duniya da take samar da makamashin Uranium sai dai kuma kampanin samar da makamashin nukiliyan Areva na Kasar Faransa da yake aiki a Nijar din na rasa karfin ikon da yake da shi a fannin hakar ma'adanin a daidai lokacin da Gwamnatin Nijar ke kokarin ganin ta ja hankalin wasu Kamfanonin domin su zuba jari a harkar ta Uranium.
Kasashen yamma dai na ganin Iran na kokarin karfafa dangantakar makamashin Uranium ne da Nijar, sai dai kuma Ministan harkokin wajen Jamhuriyyar ta Nijar Bazoum Mohamed yace babu batun Uranium cikin abubuwan da zasu tattauna duk kuwa da yan iya shiga ciki sai dai zasu kulla dangantakar Kasuwanci ne da Iran din.
Bayan ya kammala ziyarar sa a Nijar Ahmadinedjad zai kai makamanciyar wannan ziyara zuwa Kasar Ghana dake da arzikin man Fetur.