Shugaba Merkel na ziyarar Gabas Ta Tsakiya
June 21, 2018Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Gabas Ta Tsakiya inda za ta je kasashen Jordan da kuma Lebanon.
A yayin ziyarar Merkel za ta gana da sarki Abdallah na Jordan da kuma Firaministan Lebanon Rafik Hariri.
Tattaunawar ta su za ta mayar da hankali kan fannoni da suka hada da Ilmi da zuba jari da kuma batun 'yan gudun hijira.
Dubban daruruwan yan gudun hijirar Siriya ciki har da wadanda Jordan ta tsugunar sun yi kaura zuwa kasashen Turai musamman ma Jamus.
Batun 'yan gudun hijirar dai ya haifar da sabani a kawancen jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da takwararta ta CSU.
A ranar Lahadi mai zuwa shugabannin kasashen Turan za gudanar da taro domin tattauna mafita ga matsalolin yan gudun hijirar.