Jamus da Turkiya sun hada kai kan 'yan gudun hijira
October 18, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar Lahadin nan ta tattauna da shugabanni a ƙasar Turkiya inda ta sake jaddada buƙatar ƙasashen na Turai wajen ba da tallafi ga ƙasar yayin da ita kuma za ta yi ƙoƙari ta hana 'yan gudun hijira masu ratsa iyakar kasarta zuwa kasashen na Turai.Shugabar dai ta tattauna da Firaminista Ahmet Davutuglu da shugaba Recep Tayyip Erdogan yayin da wannan ziyara da ke zuwa a daidai lokacin da ake samun sabbin dubban 'yan gudun hijira da bakin haure na zuwa kasashen.
Cikin abin da Ƙungiyar ta EU dai ta ƙudiri aniyar ba wa ƙasar ta Turkiya sun hadar da tallafi da zai kai Euro miliyan dubu uku dan ƙasar ta dafawa ayyukanta na jinkai ga 'yan gudun hijira sama da miliyan biyu da ke a ƙasarta, baya ga saukaka batun samun "Visa" ga 'yan ƙasar ta Turkiya zuwa Turai sannan a sake nazari kan batun buƙatar ƙasar ta zama mamba a kungiyar ta EU.