Tattaunawar take hakkin bil Adama a China
October 29, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta gana da 'yan fafutikar kare hakkin bil Adama a ziyarar da ta kai a kasar China kamar yadda mai magana da yawun shugabar ya bayyana a ranar Alhamis din nan.
Shugaba Merkel ta gana da mambobi na kungiyoyin kare hakkin jama'a da lauyoyi da marubata a taskar Blog a intanet a cewar Steffen Seibert.
Mista Seibert duk da cewa bai yi cikakken bayani ba kan tattaunawar shugabar da 'yan fafutikar ya ce shugaba Merkel ta samu tattaunawa da su kan abubuwa da suka shafi dimokradiya da kare hakkin bil Adama .
Wannan kasa dai ta China mai bin tsari na Kwaminisanci a lokuta da dama na gallazawa ga 'yan fafutika inda ake daure su a gidajen kaso.
A ziyar da ya kai birnin Washington a karshen watan Satimba shugaba Xi Jinping na China ya sha kakkausar suka daga takwaransa na Amirka Barrack Obama kan batutuwa da suka shafi kare hakkin bil Adama a kasar ta China.