Hakan Shugaba Nkurunziza na Burundi ya cimma ruwa.
July 24, 2015Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya lashe kujerar shugabancin kasar a karo na uku bayan da aka gudanar da babban zaben kasar mai cike da rudani. Tun dai bayan da Nkurunziza ya yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin kasar ta Burundi a karo na uku kasar ta shiga cikin rudu inda 'yan adawa suka bayyana tsayawar ta sa da cewa ta saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar, wannan dalili ne ma ya sanya suka kauracewa zaben. Ko da ya ke Nkurunziza ya lashe zaben da gagarumin rinjaye yana fuskantar yiwuwar kauracewa da ma takunkumi daga al'ummomin kasa da kasa. Tuni dai Amirka da kungiyar Trayarfra Turai EU da ke zaman na sahun gaba a taimakon Burundin suka yi barazanar dakatar da duk wani tallafi da suke bata da ma na kakaba mata takunkumi bayan da Nkurunziza ya toshe kunnuwansa daga bukatar dakatar da aniyarsa da aka yi masa. Rahotanni sun nunar da cewa Nkurunziza ya lashe zaben da sama da kaso 69 cikin 100 na sakamakon da tuni shugaban jam'iyyar adawa ta FRODEBU Frederic Bamvuginyumvira ya ce sunyi watsi da shi.