Shugaba Obasanjo ya ba da umarnin gudanar bincike a fashewar bututun mai a Legas
May 13, 2006Talla
Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike akan fashewar bututun mai da ya auku jiya a kusa da birnin Legas. Fashewar bututun a kusa da kauyen Ilado mai tazarar kilomita 45 gabas da birnin Legas, ya halaka mutane akalla 200. ´Yan sanda sun ce kauyawa ke satar mai daga wani bangaren bututun dake yoyo lokacin da gobara ta tashi kuma kafin kace kwabo ta kama wurin baki daya. Sau da yawa dai talakawa a Nijeriya kasar da tafi arzikin man fetir a nahiyar Afirka, kan lalata bututun mai don satar mai din wanda suke amfani da shi wajen girki ko kuma sayarwa a kasuwannin baan fage. Akalla mutane dubu 2 ne suka rasa rayukansu sakamakon irin wadannan hadurra na fashewar bututun mai a tarayyar ta Nijeriya a cikin shekarun baya bayan nan.