1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Putin na ziyara a Mariupol

March 19, 2023

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya kai ziyarar ba zata zuwa birnin Mariupol da kasarsa ta mamaye. Ziyarar da ke kasancewa ta farko da shugaban ya kai zuwa yankin Donbas na Ukraine.

https://p.dw.com/p/4OtdR
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin Hoto: Russian Presidential Press Office/Kremlin/Sputnik/REUTERS

A karon farko tun bayan kaddamar da mamaya a Ukraine, shugaba Vladmir Putin na Rasha ya kai ziyara yankin Donbas da dakarunsa suka mamaye. Ziyarar na zuwa ne bayan wata da ya kai yankin Crimea a jiya Asabar, kwana guda bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta tura da sammacin kama shi. 

Kakafen yada labaran Rasha sun ruwaito cewa ya kewaya birnin Mariupol cikin mota tare da zantawa da mazauna yankin. Birnin na Mariupol da ya fada hannun Rasha a watan Mayun bara na kasance nasara ta farko da Rashar ta samu bayan da ta gaza kwace Kyiv babban birnin Ukraine. Kafafen yada labaran kasar sun kuma ruwaito cewa, shugaba Putin zai gana da babban hafsan sojan rundunarsa na Ukraine.