Shugaba Tinubu ya ja hankali kan zanga-zanga
August 5, 2024Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kiran masu zanga-zanga a kasar da su dakatar da boren da suke yi a kan tsadar rayuwa tare da shawartar su da zu so domin zama kan teburin tattaunawa.
A cikin jawabin da ya yi wa kasa a dazu-dazun nan, Shugaba Tinubu, ya ce ya ji takaicin tarzomar da ta kasance cikin zanga-zangar inda ta kai ga asarar rayuka a jihohin Borno da Kano da Jigawa da Kaduna da ma sauransu, tare da mika jajensa.
Shugaban na Najeriya ya yi zargin 'yan siyasa da rura wutar rikicin da aka shiga, yana mai bai wa matasa shawarar da kada su kyale a zuga su su rusa tsarin dimukuradiyya da Najeriya ta yi nasarar ginawa shekaru 25.
Tinubu ya ce matakinsa na janye tallafi da sauye-sauye a fannin hada-hadar kudaden waje, ya samo asali daga rashin kula da tattalin arzikin kasar tsawon shekaru.
Ya kuma ce Najeriya ta adana Naira Tiriliyan biyu daga janye tallafi da ya yi.
Sai dai kuma ba lallai ba ne 'yan Najeriya da dama su gamsu da jawabin na shugaban kasar ba, saboda kauce wa bukatarsu ta dawo da tallafin mai da Tinubu ya yi da shi ne makasudin zanga-zangar