Shugaba Trump ba zai halarci rantsar da Biden ba
January 8, 2021Talla
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a ne ya tabbatar da cewa ba zai halarci taron rantsar da shugaba mai jiran gabo Joe Biden ba. Sakon dai na zuwa ne bayan faifan bidiyon da ya fitar na nuna rashin jin dadinsa kan harin da magoya bayansa suka kai kan gini majalisar dokokin kasar wanda jawaban nasa ke kama da amincewarsa da shan kaye a zaben.
Idan har ikrarin nasa ya tabbata shugaba Trump zai kasance shugaban kasar na 2 bayan Andrew Johnson da ya ki halartar taron rantsar da magajin shi.