1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Shugaba Trump zai shata makomar TikTok a Amurka

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
January 16, 2025

Sabon zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, zai kafa sabuwar doka kan makomar Tiktok a Amurka bayan an rantsar da shi kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/4pC1U
Hoto: Antonin Utz/Seth Wenig/AFP

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump na duba yiwuwar rattaba hannu kan wata dokar da za ta shata makomar Tiktok a Amurka. Jaridar Washington Post ta ruwaito cewar mai yiwuwa Donald Trump ya kai ga daukar matakin hana amfani da manhajar ko kuwa ya hana a sayar da kamfanin a tsawon kwanaki 60 zuwa 90 bayan ya yi kome a fadar White House kan kujerar mulki.

Ba tun yau ba dai ake ta kai ruwa rana tsakanin kamfanin Tiktok mallakar China da gwamnatin Amurka, wacce ke zargin China da fakewa da manhajar wajen tatsar labarai na sirri a kasar, zarge-zargen da kamfanin ya sha musantawa.