Shugaba Yoon ya ki bayar da kai bori ya hau— Masu bincike
January 15, 2025Hukumar yaki da cin haci da rashuwa a Koriya ta Kudu ta ce tsohon shugaban kasar Yoon Suk Yeol na kin bayar da hadin kai wajen yin magana bisa tuhume-tuhumen da ake yi masa. Jami'an hukumar sun yi wa shugaban dirar mikiya a tsakiyar gidansa inda ya ja daga, inda ya shafe tsawon kwanaki yana kulli-kurciya da jami'an tsaro da ke kokarin kama shi.
Karin bayani : An gaza kama shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige
An ruwaito cewar da kyar da jibin goshi ne 'yan sandan da suka samu zarafin kutsawa a wajen da yake boye suka cafko shi da karfin tuwo. Amma Shugaba Yoon mai shekaru 64 da aka zarga da yunkurin dagula dimukuradiyya ta hanyar kafa dokar ta-baci a kasar Koriya ta kudu gabanin tsige shi, ya ce ya mika wuya ne ga jami'an bincike saboda gudun a zubar da jini
Karin bayani : Tshon shugaban Koriya ta Kudu na bijire wa yunkurin kama shi
Yoon Suk Yeol ne zai kasance shugaban farko a kasar Koriya ta Kudu a tarihi da jami'an tsaro suka kama bayan kada kuri'ar tsege shi a tsakiyar watan jiya.