1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Zelensky na ziyara a yankin Baltic

January 11, 2024

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce, yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yaki da Rasha ba za ta haifar da tattaunawa a siyasace ba face kawai ta amfani gwamnatin Moscow.

https://p.dw.com/p/4b7xp
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr ZelenskyHoto: AFP/Getty Images

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Estonia a ziyarar da ya fara a yankin Baltic, shugaba Zelensky ya ce duk wani jan kafa ka iya zama kasadar da za ta bayar da dama ga Rasha ta sake daura damara da kuma ninka samun makamai

Karin bayani: Rasha: Putin ya sanar da nasara a yakin Ukraine    

A ziyararsa zuwa kasashen Lithuania da Latvia da kuma Estonia, shugaba Zelensky na fatan kara matsa lamba ga kawayensa na yammacin Turai domin samun karin tallafin makamaki tare da tattauna yunkurin shigar Kyiv cikin kungiyoyin kawancen tsaro ta NATO da kuma Tarayyar Turai EU.