Shugaban ƙasar Faransa na tattaunawa da Angela Merkel
October 19, 2011Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya yadda zango a birnin Francfort da ke a nan tsakiyar ƙasar Jamus;inda zai halarci wani taron gauggawa na share fage ga babban taron ƙungiyar Tarrayar Turai da za a gudanar ran lahadi a birnin Brussels na ƙasar Beljium domin tattauna matsalar tattalin arziki da ƙasashen ƙungiyar ke fama da ita.
Sarkozy wanda zai sadu da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel a birnin na Francfort inda nan ne cibiyar banki Tarrayar Turai tare kuma da wasu sauran hukumomin kudi na ƙungiyar.Zasu tsara shirin da za su gabatar ga babban taron da za a yi nan gaba domin samar da hanyoyin da za su zama mafita ga rikicin kuɗi na ƙasashen.Tun can da fari a taron da shugabannin biyu suka yi a birnin Berlin Merkel da Sarkozy sun yi alƙawarin gabatar da sahihan shawarwari ga babban taron na ƙungiyar Tarrayar Turai.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Moahammed Abubakar