1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ƙasar Laberiya na kai ziyara Birtaniya.

May 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuwG

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kasar Laberiya, ta isa a birnin London, don fara wata ziyarar kwana uku a Birtaniya, inda za ta yi shawarwari da jami’an gwamnati, sa’annan ta kuma gana da Sarauniya Elizabeth ta biyu. Shugaba Sirleaf, wadda ita ce farkon shugaba mace ta wata ƙasa da aka taɓa zaɓa, a tarihin nahiyar Afirka, ta iso Birtaniyan ne, bayan wata ziyarar da ta kai a Amirka. A ran laraba ne dai za ta gana da Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, sa’annan kuma ta yi shawarwari da Sakatariyar kula da ba da taimakon raya ƙasashe ta Birtaniya, Hilary Benn da kua ministan harkokin Afirka, Lord Triesman. Ana dai kyautata zaton cewa, a lokacin ziyarar, shugaba Sirleaf za ta bukaci Birtaniya ta ba da ƙarin gudummowa wajen sake gina ƙasarta, Laberiya.