Shugaban Afghanistan ya fice daga kasar
August 15, 2021Talla
Kungiyar Taliban na jiran a mika mata ragamar mulkin Afghanistan. Tuni dai shugaba Ashraf Ghani ya fice daga kasar tun bayan da mayakan Taliban suka sami nasarar kutsawa birnin Kabul, suna masu ikrarin sake karbar ikon kasar bayan shekaru 20 da sojojin kasa da kasa suka kwace mulki a hannunsu.
Kawo yanzu dai ba a san inda shugaban kasar yake ba.
Mukadashin ministan harkokin cikin gida na kasar Abdul Sattar Miryakawal ya ce za a mika ragamar mulkin kasar ga gwamnatin rikon kwarya.