1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Shugaban Amirka ya nemi ganin kawo karshen rikicin siyasa

January 8, 2021

Shugaba Donald Trump na Amirka mai barin gado ya nemi al'umar kasar da su sasanta juna, bayan zaben shekarar da ta gabata ta 2020, da kalubale musanman annobar corona ta halaka mutane masu yawa.

https://p.dw.com/p/3ngdD
USA Donald Trump und Mike Pence
Hoto: Carlos Barria/REUTERS

Wannan kira na mayar da zukatu nesa da kwantar da hankula da Shugaba Donald Trump ya yi kwana daya bayan da wasu ‘yan ta'adda na siyasa  magoya bayan Trump sun yi kaca-kaca da ginin majalisar dokokin Amirka, har suka tursasa ‘yan majalisar buya don tsira da rayukansu lokacin da suke aikin tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ta 2020, tamkar fargar jaji ce da borin kunya, duba da irin abubuwan da ya fada.

Rikidewar da wannan gangami ya yi zuwa tashin hankali ya sa ake ganin cewa kusan duk abubuwan da Trump ya fada masu kama da ihu bayan hari ne, kuma karya ce kawai. Ana kuma musanta ikirarin da ya yi cewa nan take ya kira dakarun tsaron cikin kasa, musanman ganin yadda faya-fayin bidiyo suka tabbatar da yadda ‘yan dabar masu goyon bayan shugaban, suka ci karfin ‘yan sandan majalisar.

USA | Präsidentschaftswahl | Demonstranten im Capitol
Hoto: Lev Radin/Pacific Press/picture alliance

Karin Bayani: Zaben Amirka: Al'umma cikin zaman dar-dar

Shugaban wanda ya ce zai ci gaba da fafatukar ganin an aiwatar da sauye-sauye a tsarin zaben Amirka domin tabbatar da sahihancin masu kada kuri'a, ya yi kokarin wanke kansa daga ta'asar da magoya bayan suka tafka.

A halin da ake ciki dai, an damke mutane fiye da 80 da ake zargi wajen ta'asar da aka yi a ginin majalisar dokoki, yayin da hukumomin tsaro suka yi tayin ba da tukuicin dala dubu daya, kwatankwacin naira dubu 450, ga duk wanda ya taimaka da bayanan cafke wasu tsegaru hudu da ake nema. Magajin birnin Washington, Madam Mauren Bauza ta yi kira ga jama'a da su ci gaba da harkokin yau da kullum cikin bin doka da lumana.