1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bolsonaro: Corona ba ta da tasiri a kan 'yan kwallo

May 31, 2020

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya ce yana son ganin kasarsa wace ta shahara a bangaren kwallon kafa a duniya ta dawo da buga wasannin a cikin gida.

https://p.dw.com/p/3d3lf
Brasilien Coronavirus Jair Bolsonaro
Hoto: Getty Images/A. Anholete

Shugaban na wannan furuci ne duk kuwa da cewa kasar a yanzu ta shiga cikin kasashen da coronavirus tafi kamari.

Kawo safiyar Lahadin nan alkaluma na nuna cewa kasar ta Brazil ta samu masu corona kusan 500,000, kasar kuma ita ce kasa ta biyar a jerin kasashen da cutar tafi yin kisa a duniya, inda a yanzu Brazil ta zarta Spain samun wadanda corona ta hallaka.

To amma duk da haka, Jair Bolsonaro, Shugaban na Brazil wanda tun farko ya rinka nuna tababa a kan wanzuwar coronavirus, ya ce yana son a dawo da wasanni domin akasarin 'yan wasa matasa ne a saboda haka koda sun kamu da corona, cutar ba za ta kashe su ba. Kazalika Bolsonaro ya ce babban abin da ya sa yake son a dawo da wasanni shi ne domin a samar da aikinyi a saboda ya san irin radadin da ke tattare da mutum ya zauna baya aikin komi.