Gwamnatin Burkina Faso za ta magance matsalolin tsaro
November 26, 2021Talla
Shugaba Roch Marc Christian Kabore na kasar Burkina Faso ya sha alwashin daukan matakan da za su magance matsalolin tsaron da kasar take fuskanta na hare-hare daga tsagerun masu dauke da makamai da ke ikirarin jihadi, inda jami'an tsaro da dama suka rasa rayukansu.
Shugaban ya ce gwamnatin za ta kara ba da kula ga sojojin kasar. Tun shekara ta 2015 hare-haren sun halaka kimanin mutanen dubu-biyu yayin da wasu kimanin milyan daya da rabi suka tsere daga gidajensu.
Kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka tana sahun gaba na kasashe masu fama da talauci.