Shugaban Chadi ya ziyarci Isra'ila
November 25, 2018Talla
Shugaba Idriss Debyn ne dai shugaba na farko daga kasashen tsakiyar Afirka da ya ziyarci Isra'ilar tun samuwarta a shekara ta 1948, ziyarar kuwa da ofishin Mr. Netanyahu ya ce ta tarihi ce.
A shekara ta 1972, Chadi wadda galibin al'umarta musulmi ne, ta yanke huldar diflomasiyya da Isra'ila.
Tun cikin shekara ta 2016 ne dai firaminitan na Isra'ila ya mike tsaye don ganin ya kyautata huldar kasarsa da kasashen nahiyar Afirka da dama, ciki har da Kenya da Yuganda da Ruwanda da kuma Habasha.
Isra'ilar ta kuma taba alkawarin taimaka wa kasashen Afirka da yaki da ta'addanci, musamman ta fuskar bayanan sirri.