Shugaban Turkiyya zai gana da Shugaban Hamas
April 20, 2024Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya ne ganawa da shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinu, Ismail Haniyeh a birnin Santanbul domin tattauna halin rikicin da Zirin Gaza ke ciki.
Sai dai ba a bayyana karin bayani kan yanayin da tattaunawar za ta kasance ciki ba tsakanin bangarorin biyu. A ranar Larabar da ta gabata ce dai, Haniyeh ya gana da ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan a Qatar kan batun tsagaita bude wuta a Zirin da kuma sakin wadanda aka tsare da su.
A farkon wannan makon ne dai Shugaba Erdogan dai ya soki Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a kan abun da ya bayyana a matsayin kisan kiyashi a Gaza. Sai dai kuma Isra'ila ta nisanta kanta da kalaman shugaban.
Ko da yake duk da zafafan kalaman na Shugaba Erdogan, a baya-bayan nan Turkiyar ta yi kokarinta na shiga tsakani domin sasanta rikicin na Gaza.